Bayanin ya bayyana manufa da matakan da Sin ke dauka a fannoni bakwai, wato kara samun fahimtar juna a fannin siyasa, da karfafa hadin gwiwa a fannonin harkokin kasa a kasa, da tattalin arziki da kuma cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka, da zurfafa mu'amala da hadin gwiwa a fannin al'adun bil'adam, da sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka, da kara yin mu'amala da hadin gwiwa a fannonin diflomasiya da harkokin shari'a da dai sauransu.
A shekarar 2006 ne gwamnatin kasar Sin ta fara fitar da bayanai game da manufofinta kan nahiyar Afirka. A cikin shekaru 10 da suka wuce, an aiwatar da dukkan abubuwa dake kunshe cikin bayani yadda ya kamata, wanda ya taimaka matuka wajen raya dangantaka tsakanin bangarorin biyu a duk kan fannoni.(Fatima)