Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya bayyana cewa bayan sauraron jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping, jawabin na kunshe da ma'ana sosai ta hanyar gudunmuwar da za ta bayar a kusan ko wane bangare. Ya ce yayi imanin cewa za'a amince da yin jinjina na musamman ga Shugaban na kasar Sin.
Ya lurar da cewa, Mr Xi yana wakiltar kasa ce da a baya ake mata kallon talauci, kasar da ba'a taba mata mulkin mallaka ba. Ga shi ya zo yana yi ma kasashen Afrika abin da kasashen da suka yi mulkin mallakan ya kamata a ce su ne suka yi.(Fatimah Jibril)