Shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda yake halartar babban taron hadin gwiwwa tsakanin Sin da Afrika, ya kira wani taron da shugabannin kasashen Afrika 13 a ranar Jumma'ar nan a cigaba da ake na taron hadin gwiwwa na FOCAC domin tattauna dabarun samun cigaba.
Shugaba Xi a cikin kasashen da ya gana da shugabanninsu sun hada da Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo, Uganda, Komoros, Sudan ta Kudu, Morocco, Rwanda, Botswana da dai sauransu.
A wajen ganawar ya shaida musu cewa, ziyararsa a nahiyar tana da manufa biyu. Na farko domin ya jagoranci taron Johannesburg na hadin gwiwwa tsakanin Sin da Afrika wato FOCAC tare da shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma, sannan a daya hannun kuma domin tattauna dabarun samun ci gaba da shugabannin kasashen Afrikan da suka halarci taron.
Mr. Xi ya gabatar da tsarin tattalin arzikin Sin ga shugabannin na Afrika, da kuma aniyar da kasar ta yi kwanann nan na muradan cigaba, dabaru da inda ta maida hankali, yana mai jaddada cewa kasar Sin a shirye take ta kara bada gudummawarta ga cigaban nahiyar, kuma tana maraba da kasashen nahiyar da su samu habaka tare da ita.
Shugabannin kasashen Afrikan da suka halarci taron sun jinjina ma muhimmancin da Sin ta dora a kan nahiyar ta Afrika, suna masu cewa idan har ana son samun cimma ganin masana'antu da kayayyakin aikin gona na zamani, kasashen nahiyar suna bukatar matsanta hadin gwiwwa da kasar Sin.
Sun lura da cewa shirin ziri daya da hanya daya na kasar Sin yana da muhimmanci ga nahiyar ta Afrika, sun yi maraba da ayyuakn da Sin take yi a bangaren hanyar dogo, hanyoyin mota, gidan tashar jiragen ruwa a nahiyar, sannan kuma da kokarin da take yi na taimaka ma nahiyar wajen samar da kayayyakin gina kanta.(Fatimah Jibril)