A ranar Talatar nan, gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, ana samun karuwar yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV ko AIDS a tsakanin mutanen dake aikata luwadi a wannan kasar da ke yammacin Afrika.
A wata kididdiga da ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta fitar ta nuna cewar, yaduwar cutar ta HIV a tsakanin jinsin maza dake aikata luwadi ya kai kashi 22.9 cikin 100, wanda ya zarta na masu aikata zina wanda ya kai kashi 19.4 cikin 100.
Wannan kididdiga ta nuna cewar, an dan samu raguwar yaduwar cutar ta AIDS a tsakanin mata masu zaman kansu a kasar.
A yayin da Najeriya ta bi sahun kasashen duniya na gudanar da bikin yaki da cutar ta AIDS, wanda a kan gudanar a Abuja, babban birnin kasar, gwamnatin kasar ta ce, a halin yanzu adadin mutanen dake dauke da cutar a fadin kasar ya kai miliyan 3, amma daga cikin adadin, mutane dubu 800 ne ke zuwa asibiti don duba lafiyarsu.
Taken yaki da cutar a Najeriya na wannan shekara shi ne, kawar da cutar AIDS nan da shekara ta 2030.
Karamin ministan ma'aikatar lafiyar kasar Osagie Ehanire, ya ce, za'a iya rage kaifin cutar ta AIDS a Najeriyar ta hanyar rage radadin talauci da kuma samar da muhimman bayanai da suka danganci cutar.(Ahmad Fagam)