Masu sharhi kan al'amurran tattalin arziki a Najeriya sun ce, akwai kyakkyawar fata game da matakin da babban bankin kasar CBN ya dauka na rage adadin kudin ruwa a sha'anin hada hadar kudaden kasar da cewar matakin zai taimaka wajen janyo hankulan masu zuba jari a kasuwannin hannayen jarin kasar.
Shugaban sashen kudi da al'amurran bankuna na jami'ar jihar Nasarawa Uche Uwaleke, ya ce, matakin da babban bankin kasar ya dauka na zaftare kudin ruwa daga kashi 13 cikin 100 zuwa kashi 11 cikin 100 zai matukar habaka kasuwar hannayen jarin kasar da kuma janyo hankulan masu zuba jari a fannin.
Uwaleke, ya fadi hakan ne a ranar Larabar nan a Abuja cewar, matakin da babban bankin ya dauka zai ba da dama ga manya da kananan 'yan kasuwa wajen samun rance, domin bunkasa harkokin kasuwancinsu da kuma samar da guraben ayyukan yi, sannan a cewar sa wannan labari ne mai armashi ga kamfanoni.
A nasa bangaren, babban jami'i a cibiyar lura da al'amurran kudi ta Najeriya Godwin Echoi, ya ce, wannan mataki zai ba da damar fadada ci gaban tattalin arziki, musamman ta hanyar zuba jari a fannonin aikin gona da ma'adanai, kuma dama an jima ana sa ran bankin na CBN ya dauki wannan matakin.(Ahmed Fagam)