Mahukunta a Najeriya na daukar karin matakan tsaro a filayen tashi da saukar jiragen sama, a wani mataki na kandagarkin aukuwar hare-hare a lokutan bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara.
Mai magana da yawun hukuma mai lura da filayen jiragen saman kasar wato FAAN Yakubu Dati, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, rundunar 'yan sandan kasar ta girke na'urorin gano ababen fashewa a daukacin filayen jiragen saman kasar, domin tabbatar da wannan aiki.
Dati ya ce, hakan kari ne kan irin matakan da jami'an hukumar ta FAAN ke dauka wajen tabbatar da tsaro a filayen jiragen, ciki hadda sanya na'urorin binciken jikin fasinjoji irin na zamani, da ma wadanda ke iya bayyana makaman da aka sakaye a jiki.(Saminu)