in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta kara sace wasu kananan 'yan mata a Najeriya
2015-12-01 09:58:45 cri

Wasu karin kananan 'yan mata sun sake fada wa hannun Boko Haram a wani harin baya bayan nan da mayakan kungiyar suka kai ga wani kauyen jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, in ji wasu majiyoyin tsaro da mazauna wurin a ranar Litinin.

An sace wani adadi da ba a tantace ba na kananan 'yan mata a ranar Lahadi da safe a kauyen Bam, dake nisan kilomita 170 daga kudancin Maiduguri, hedkwatar jihar Borno, inda kuma maharan suka lalata gine gine da kashe mutane a kalla bakwai, a cewar wani jami'in tsaro da ya bukaci a sakaya sunansa.

Kakakin 'yan sandan jihar Borno, Victor Ikuku, ya jaddada cewa, babu wasu bayanan da ya samu game da sace 'yan matan.

Ali mallam Ali, wani basaraken kauye, ya bayyana cewa, yawancin mazauna suna barci a lokacin lamarin ya faru. Maharan sun tattara dukkan matan kauyen, kana suka raba matan aure da kananan 'yan mata kafin su tafi da su, in ji wannan basaraken.

Wani mazaunin ya bayyana cewa, labarin sace 'yan matan ya tada hankalin mutanen jihar Borno matuka, musammun ma ganin cewa 'yan matan makarantar Chibok fiye da 217 da aka sace a shekarar bara har yanzu ba a gano ina suke ba.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari dai, ya yi alkawarin maido da wadannan 'yan mata ga iyayensu, sai dai kuma ana fargabar cewa, wasu daga cikinsu, an tsallaka da su zuwa wasu yankunan ketare, ko ma an auratar wasu daga cikinsu ga mayakan Boko Haram. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China