An sake bude makarantu a jahar Borno dake arewacin Najeriya a ranar Talatar nan, bayan shafe sama da shekara guda makarantun na rufe sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram.
Kafin sake bude makarantun dai, gwamnatin jihar Borno ta bukaci iyayen yara su tura 'yayan su makarantun, duk da irin fargabar dake zukatan al'umma na yawaitar hare hare daga kungiyar mai ikirarin kishin Islama.
Musa Kubo, kwamishinan ilmin jihar Borno ya ce, akwai tabbaci dangane da samar da tsaro a makarantun jihar.
A tsawon lokutan da makarantun jihar suka kasance a rufe, an yi amfani da su ne wajen ba da mafaka ga mutanen da hare haren Boko Haram suka daidaita.(Ahmed Fagam)