in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hafsan sojin Najeriya ya ce za su murkushe Boko Haram
2015-11-25 09:56:54 cri

Babban hafsan rundunar sojin Najeriya laftanal Janar Tukur Buratai, ya fada a ranar Talatar nan cewar, sannu a hankali za su ga bayan kungiyar Boko Haram, sakamakon irin nasarorin da sojin kasar ke samu a yakin da suke da kungiyar.

Ya ce, a halin da ake ciki yanzu, sojojin kasar ba su kai ga ainihin wajen da suke son kaiwa ba, amma da sannu za su kai wuraren, kuma sojojin suna samun galaba.

Buratai, ya fadi hakan ne a yayin da ya ziyarci runduna ta 72 ta dakaru na musamman na sojojin kasar dake Makurdi, babban birnin jihar Benue dake shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya.

Ya ce, tabbas, sojojin Najeriya suna samun galaba a yaki da kungiyar Boko Haram cikin kankanin lokaci. Ya kara da cewar, a 'yan kwanakin nan sojojin Najeriya sun samu nasarar damke wasu daga cikin kwamandojin kungiyar Boko Haram, sannan sun ragargaza sansanonin kungiyar da dama, da kuma wuraren hada boma bomai na kungiyar a yankunan jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.(Ahmed Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China