in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Najeriya ta karyata batun bacewar dakarun ta
2015-11-20 10:04:53 cri
Rundunar sojin Tarayyar Najeriya ta karyata wasu rade-radi dake cewa wasu dakarun rundunar 105 sun yi layar zana, bayan wata kafsawa da suka yi da mayakan Boko Haram.

Da yake karin haske game da hakan, mai magana da yawun rundunar manjo janar Yusha'u Abubakar, ya ce dakarun sojin kasar sun yi dauki ba dadi da mayakan Boko Haram tare da karbe garin Gulumba dake jihar Borno, kuma suna ci gaba da rike wannan gari.

Manjo janar Yusha'u Abubakar ya kara da cewa, sojojin na ci gaba da daukar matakan kakkabe ragowar magoya bayan kungiyar 'yan ta'addan dake boye a yankin.

Yanzu haka dai dakarun Najeriya da hadin gwiwar takwarorin su na Chadi, da Nijar da Kamaru, na ci gaba da kafsawa da dakarun Boko Haram a sassan Arewa maso Gabashin kasar, a daidai gabar da kuma ake samun karuwar hare-haren kunar bakin wake a wasu sassan kasar, ciki hadda harin ranar Laraba a kasuwar waya dake jihar Kano.

Tun daga shekarar 2009, lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram suka fara kaddamar da hare-hare kawo yanzu, kungiyar ta hallaka mutane da yawan su ya kai 13,000, tare da garkuwa da wasu daruruwan fararen hula a Najeriya, da Nijar, da Kamaru da kuma Chadi. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baiwa rundunar sojin kasar wa'adin watan Disambar dake tafe da su tabbatar sun ga bayan kungiyar ta Boko Haram.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China