A ranar Talatan nan Manzon Musamman na Magatakardar MDD a yammacin Afrika ya isa birnin Ouagadougou domin ganawa da zababben shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, kamar yadda kakakin MDD ya shaida ma manema labarai.
Mohamed Ibn Chambas, manzon na MDD ya kuma gana da shugaban hukumar zaben kasar mai zaman kanta da kuma wakilan kungiyar tarayyar Turai da na kungiyar tarayyar kasashen Afrika wadanda suka je aikin sa ido a zaben, in ji Stephane Dujarric, kakakin MDD a lokacin da yake bayani ma manema labarai.
Bisa kwarya-kwaryar sakamakon zaben da aka sanar, Mohamed Ibn Chambas ya taya al'ummar kasar ta Burkina Faso murna, kungiyoyin fafutuka na jama'a, gwamnatin wucin gadi, hukumar zaben da duk sauran masu ruwa da tsaki a fagen siyasa bisa nasarar zaben.
Manzon na MDD ya lura da cewa, zaben ya kawo karshen gwamnatin wucin gadi a kasar kuma MDD da sauran kasashen duniya baki daya suna tare da Burkina Faso a wannan sabon zamani.(Fatimah I. J.)