in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardan MDD ya yi kira da a gudanar da zabe cikin lumana bayan juyin mulki a Burkina Faso
2015-10-06 14:21:36 cri

Babban magatakardan MDD ya yi kira da a gudanar da zabe kafin lokacin da aka shirya a kasar bayan yunkurin juyin mulki da sojoji suka yi a watan gabata a kasar

 

Da yake ganawa da Micheal Kafando shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar a wannan rana, Mr Ban ya bayyana juyayin shi ga iyalan wadanda suka rasu ko suka ji rauni a sakamakon juyin mulkin da ya faru a ranar 16 ga watan satumba, kamar yadda kakakin majalissar ya bayyana a cikin wata sanarwa.

 

Sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin sun tsare Mr Kafando na dan wani lokaci

 

Babban magatakardan da Mr Micheal Kafando sun yi musayar ra'ayi a kan yanayin da ake ciki a kasar ta Burkina Faso, inda Mr Ban ya jaddada kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su nuna halin dattaku kana su yi kokari su yi hakuri kuma su yi aiki tare domin kare muradun kasar baki daya.

 

Har ila yau babban magatakardan ya jaddada goyon bayan majalissar a kokarin da kasar take yi da suka hada da shirya babban zabe. A dangane da hakan kuma Mr Ban ya sake nanata cewa yana da muhimmancin idan aka gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalissun dokoki cikin kwanciyar hankali da lumana .

 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China