Yanayin tattalin arziki da na al'umma a kasar Burkina Faso har yanzu na cikin rauni, shekara guda bayan kifar da tsofuwar gwamnatin kasar, a cewar wani rahoto na ma'aikatar dake kula da tattalin arziki da aka fitar a ranar Asabar 31 ga watan Oktoba.
Binciken da aka gudanar jim kadan kafin yunkurin juyin mulki na ranar 16 ga watan Satumban da ya wuce a cikin wani rukunin jama'a 985 da aka yi binciken kansu a birnin Ouagadougou, hedkwatar kasar ya nuna cewa, yanayin tattalin arziki da na jama'a na cikin rauni har yanzu, makwanni kalilan a kawo karshen mulkin wucin gadi.
A cikin rahoton, kashi 58 cikin 100 na mutanen da aka yi ma bincike ya nuna cewa, yanayin zaman al'umma na cikin matsatsi har yanzu, a yayin da kashi 34 cikin 100 suke bayyana kyautatuwar yanayi, kana kuma kashi 33 cikin 100 suke ganin dorewar zaman lafiya. (Maman Ada)