Idan wadannan jam'iyyun siyasa, a karkashin hedkwatocinsu aka tabbatar suna da hannu, to hakan zai kai ga tsige su kwata kwata daga fagen siyasa, in ji Rene Bagoro, alkali kuma ministan muhalli na gwamnatin wucin gadi a yayin wani taron manema labarai.
A cewar alkali Rene Bagoro, jam'iyyun siyasa ana daukarsu a matsayin mutane masu dattako, don haka ana iya hukunta wani mutum mai dattako idan ya aikata laifi. (Maman Ada)