Dukkan kasashen dake yankin Sahel matsalar ta'addanci ta shafe su. Dalilin haka ne ya kamata mu yi aiki tare, domin har yanzu akwai 'yan ta'adda a arewacin wannan yanki, har ma da Boko Haram, kuma suna kai hare hare a ko ina a inda suke iya kaiwa. Idan muna kara karfi cikin hadin gwiwa, ba shakka tashin hankali zai ja da baya, in ji janar Pierre de Villiers, bayan gana da shugaban rikon kwarya na Burkina Faso, Michel Kafando. (Maman Ada)