Wannan tawaga, da kungiyar shiyyar ta tura bisa tushen yarjejeniyar dake nuna fifiko kan tsarin demokaradiyya da shugabanci na gari, za a daura mata nauyi musamman ma wajen tabbatar ganin an gudanar da zabe cikin 'yanci da kwanciyar hankali da adalci. Kuma za ta kunshi masu sa ido 133, da za a tura zuwa yankunan kasar baki daya, domin su sanya ido kan yadda dukkannin ayyukan zabe za su gudana.
Bayan zaben, in ji wannan majiya, tawagar sa ido ta ECOWAS za ta iya bayyana ra'ayinta ko ma gabatar idan akwai bukata da wasu shawarwari zuwa ga dukkan masu ruwa da tsaki da zaben ya shafa. (Maman Ada)