Game da hakan, shugabar ofishin kula da shirin muhalli da makamashi na asusun kiyaye hallitun duniya(WWF) madam Samantha Smith, ta bayyana cewa a matsayin ta na kasa mai tasowa, matakan da shugaba Xi ya ambata cikin jawabinsa sun bayyana niyyar kasar ta Sin ta taimakawa sauran kasashen duniya a fannin tinkarar sauyin yanayi, matakin da ke da matukar ma'ana.
Ta ce ana fatan Sin za ta zama abin koyi ga kasashe masu sukuni, tare da kalubalantar kasashe masu sukuni, da su kara ba da gudummawa wajen taimakawa kasashe masu tasowa a fannin tinkarar sauyin yanayi.
A nasa bangare, shugaban babban taron sauyin yanayi na Lima, kana ministan muhalli na kasar Peru Manuel Pulgar-Vidal, cewa yayi Sin ta taka muhimmiyar rawa a fannin shawarwari game da yarjejeniyar sauyin yanayi. Ya ce kasashe masu sukuni ne suka haifar da wannan matsala ta sauyin yanayi, wannan ne kuma dalilin da ya sa ya kamata a dauki alhakin yin tarayya wajen warware matsalar, amma tare da banbance matsayin kasashe cikin yarjejeniyar.
A nasa tsokaci yayin taron, ministan muhalli na kasar Cote d'Ivoire, Rémi Allah Kouadio cewa ya yi, Sin muhimmiyar aminiya ce ga kasashen Afirka wajen tinkarar kalubalen sauyin yanayi. Kuma kafa asusun hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa game da tinkarar kalubalen sauyin yanayi da Sin ta yi, zai haifar da babban zarafi ga kasashe masu tasowa, kana kasashen Afirka suna maraba, da godiya ga kasar Sin kan wannan mataki. Ya kuma yi fatan ganin Sin ta zama abin koyi ga sauran kasashen duniya. (Fatima)