Mista Zuma, da ya koma kasarsa, ya bayyana cewa taron ya cimma nasarar kara zurfafa dangantaka tsakanin kasashen BRICS da kuma karfafa horon BRICS, lamarin da ke kasancewa wani babban taimako ga harkokin siyasa da na tattalin arzikin duniya.
Babu wani shakku a cikin tunanin mu, cewa kusan shekaru bakwai baya, da shigar mu a cikin kungiyar BRICS, siyasar duniya na cigaba da sauya wa kuma gungun kasashen BRICS na kawo wani muhimmin taimako musammun ma ga tattalin arzikin kasashe masu tasowa, in ji shugaban Afrika ta Kudu.
A cewar kakakinsa Harold Maloka, mista Zuma yayi amfani da wannan rangadi nasa a birnin Ufa domin gudanar da tattaunawa daban daban tare da takwarorinsa na kasashen BRICS a yayin taron. (Maman Ada)