in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya takaita nasarorin da aka cimma a yayin halartar shugaba Xi Jinping a taron BRICS da na SCO
2015-07-12 14:29:53 cri
Daga ranar 8 zuwa 10 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a birnin Ufa na kasar Rasha domin halartar taron ganawar shugabannin kasashe membobin kungiyar BRICS karo na 7 da taron majalisar shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) karo na 15. Bayan kammala wadannan taruka biyu, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani kan wannan ziyara ta shugaba Xi Jinping.

Wang ya ce, ba da gangan ba ne aka shirya wadannan taruka biyu a wuri daya da kuma lokaci daya. Tsarin kasashen BRICS da na SCO, tsarin hadin gwiwa ne musamman ma tsakanin kasashe masu karfin raya tattalin arziki da kasashe masu tasowa, kuma muhimmin dandali ne na yin hadin gwiwa da hada kai tsakaninsu a duk fadin duniya a yanzu. Shugaba Xi da sauran shugabannin kungiyar BRICS hudu da kuma shugabannin kasashen Turai da Asiya kimanin 20 suka hallara a birnin Ufa na Rasha, domin zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS, da sa kaimi ga samun karin ci gaban kungiyar, da raya muhimmiyar dangantaka tsakanin bangarori biyu, da sa kaimi ga raya ayyukan "Ziri daya da hanya daya", da tabbatar da sakamakon da aka samu daga yakin duniya na biyu, a kokarin tabbatar da tsarin duniya bisa jagorancin MDD.

An sami nasarori da dama a wadannan taruka biyu, tare da samun martani daga kasa da kasa, inda aka yi shawarwari kan tsaron siyasa da hadin gwiwar tattalin arziki, tare da cimma matsaya da dama. A cikin yini uku kawai, shugaba Xi ya halarci harkoki 25 na tarukan kolin biyu, da ganawa da shugabanni da kusoshin kasashe 7, da yin muhimman jawabai da dama, tare da daddale hadaddiyar sanarwa da yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannoni iri iri guda 23. Ana mai da hankali sosai kan wannan ziyarar shugaba Xi. Kuma ana ganin cewa, wadannan taruka biyu sun bayyana muhimmiyar rawa da Sin ta taka, kuma sun sa kaimi ga tsarin BRICs da na SCO da su samu karin ci gaba, tare da karfafa amincewa bisa manya tsare tsare tsakanin Sin da kasashen da abin ya shafa.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China