Mai rikon mukamin kakakin majalisar zartaswar kasar Phumla Williams ta shaidawa taron manema labarai a birnin Pretoria cewa, ana zargin mutane 1,123 cikin wadanda 'yan sandan suka kama da laifin zama a kasar ba tare da izni ba yayin da ake zargin ragowar da laifuffukan mallakar makamai ba bisa ka'ida ba da kuma fataucin miyagun kwayoyi.
Kakakin ta kuma ce, daga watan Afrilu zuwa Yulin wannan shekara 'yan sandan sun tantance mutane 6,781 wadanda ke jiran a tusa keyar su zuwa kasashen su. A cikin wannan adadin ana zargin mutane 1,694 da aikata manyan laifuffuka. Kuma duk wanda aka samu da laifi za a tura shi gidan kaso, kana a tusa keyarsa zuwa gida da zarar ya kammala wa'adin zaman gidan yarin.
Gwamnatin Afirka ta Kudu dai ta ce ta dauki wannan mataki ne da nufin kawar da bata gari a cikin kasar.(Ibrahim)