in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu na cigaba da kasancewa kasar da ke janyo yarin IDE
2015-08-07 10:54:54 cri

Kasar Afrika ta Kudu na cigaba da kasancewa wani muhimmin yankin da ke janyo jarin kai tsaye na waje (IDE) duk da ja da bayan kwararar shigowar yarin IDE, in ji shugaba Jacob Zuma a ranar Alhamis.

Afrika ta Kudu ta zama wani dandalin masana'antun shiyya da kuma yawan kamfanoni da suka zuba jarin wajen fadada harkokin hada hada, zamanintarwa da kuma bullo da sabbin ayyuka a wannan kasa, in ji mista Zuma a yayin wani zaman taron tambaya da amsa a majalisar dokokin kasar.

Amma shugaba Zuma ya amince cewa Afrika ta Kudu ita ma matsalar tattalin arzikin duniya ya shafe ta, dalilin haka ne kwararar shigowar yarin IDE ya ragu da dalar Amurka miliyan 8,3 a shekarar 2013. Kasar na da tsare tsare domin ingiza jari a cikin harkokin kimiyya da fasaha, ruwa da tsabta, manyan gine ginen sufuri da kamfanonin cikin gida, in ji shugaba Zuma.

Haka zalika, gwamnatin Afrika ta Kudu ta dauki niyya wajen kyautata yanayin zuba jari da kuma karfafa wasu hanyoyi domin kawo sauki ga ayyukan kasuwanci, a cewar mista Zuma, a yayin da yake bada amsa kan wasu korafe korafen 'yan majalisun adawa na zarginsa da kasa tafiyar da tattalin arzikin kasar yadda ya kamata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China