Wata sanarwa da ofishin jakadancin ya fitar ta bayyana cewa, sauran wuraren da 'yan ta'addan ke shirin kai harin sun hada da gine-ginen gwamnatin Amurkar da sauran wuraren da ke da alaka da harkokin kasuwancin Amurka. Sai dai sanarwar ba ta yi wani karin haske game da lokaci ko takamaimai wuraren da aka tsara kai wadannan hare-haren ba.
Don haka, ofishin jakadancin na Amurka ke shawartar jama'a da su sanya ido sosai a wuraren da ke kewaye da su, kana su rika bibiyar kafofin watsa labarai don karin bayani tare da bin umarnin hukumomi.
Ofishin jakadancin na Amurka ya dauki wannan mataki ne sakamakon harin ta'addanacin da aka kai rukunin shagunan zamanin nan na West Gate a birnin Nairobin kasar Kenya, harin da ake zargin 'yar kasar birtaniya mai suna Samantha Lewthwaite da kitsa shi, bayan da aka ganta tana leken asiri a rukunin ofisoshin jakandancin kasashen waje da ke kasar Afirka ta Kudu kafin kai harin.
Bayanai na nuna cewa, Samantha wadda yanzu haka ke amfani da Natalie Faye Webb, tana Afirka ta Kudu tsakanin shekarar 2008 zuwa 2011, kuma tana tafiye-tafiye da fasfon kasar Afirka ta kudu.(Ibrahim)