in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin sun jajantawa takwarorinsu na Turkiya
2015-10-12 20:50:10 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin da firaminista Li Keqiang na kasar sun aika da sakon nuna jaje ga takwarorinsu na kasar Turkiya dangane da mutane da dama suka rasu da wasu da suka jikkata sakamakon wasu bama-bamai da suka fashe a Ankara, babban birnin kasar.

A cikin sakon nasu, a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, shugabannin na Sin sun nuna juyayi ga mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyar fashewar, tare da janjantawa wadanda suka jikkata da kuma iyalan mamatan. Har wa yau sun jaddada cewa, kasar Sin na adawa da kakkausan murya da duk wani irin na'u'i na ta'addanci, kuma ta yi tir da harin ta'addanci da aka kai kan fararen hula. Kasar Sin na son hada kai da Turkiya da kasashen duniya a kokarin da ake na yaki da ta'addanci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China