Hong Lei ya fadi haka ne a yau Jumma'a 27 ga wata yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, inda aka tabo batun cewa, shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce, kasarsa na jiran Turkey ta nemi gafara ko ta biya diyya sakamakon harbo jirgin saman sojan Rasha.
Sannan kuma kakakin kasar na Rasha ya bukaci Turkiya da ta yi bayani kan lamarin. A waje daya kuma, Turkiya ta ce, ta harbo jirgin Rasha ne bisa umurni, don haka babu bukatar neman gafara daga wajen Rasha.
Hong Lei ya kara da cewa, an harbo wani jirgin saman sojan Rasha, har ma ya sa wani matukin jirgin ya rasu, lamari ne maras sa'a, kasar Sin ta tausaya lamarin. (Tasallah Yuan)