Ya zuwa yanzu babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin. A cewar wasu da lamarin ya faru gaban idonsu, lamarin fashewar boma-bomai ya faru har sau biyu a filin dake gaban tashar jirgin kasa.
Shugaban Turkiya, Recep Tayid Erdogan ya yi alla wadai da wannan hari, wanda a cewarsa yake neman kawo baraka ga hadin kan 'yan kasa.
Turkiya na shirin gudanar da zabuka a ranar 1 ga watan Nuwamba, a cikin wani yanayi na tashin hankali da rikici tsakanin jam'iyyun siyasa, wadanda suka kasa kafa wata gwamnatin hadaka a yayin zabukan watan Yuni.
Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ya yi allawadai a ranar Asabar da wannan harin ta'addanci na Ankara, tare da aike da ta'aziyarsa ga iyalan mamatan.
Haka kuma, a cikin wannan sanarwa ta kakakinsa, mista Ban ya nuna fatan ganin an gurfanar da masu hannu kan wannan hari gaban kuliya cikin gaggawa. (Maman Ada)