Luke Jordan wanda ya bayyana hakan yayin da ya ke yiwa manema labarai bayani game da dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a takaice da za a gudanar a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu. Ya ce, kamata ya yi kasashen na Afirka su kara fadada tunaninsu, maimakon dogara kan tallafin kudaden da kasar Sin take ba su.
Ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen na Afirka su yi koyi da dabarun da kasar Sin ta yi amfani da su wajen raya yankunan karkara da zuba makuden kudade a bangaren bincike a manyan makarantu da kuma kafa cibiyoyin nazari.
Shi ma wani babban jami'in bincike a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar Afirka ta kudu Romain Dittgen ya bayyana cewa, kasar Sin a shirya ta ke ta yi musayar fasahohinta da kasashen Afirka.
Jami'in ya ce, ana fatan wasu sabbin abubuwa game da dangantakar Sin da Afitka za su bullo, bayan taron kolin na FOCAC da za a yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu a watan Disamban wannan shekara.
Ya kuma yaba gudummawar dakarun da kasar Sin ta baiwa MDD wadanda a halin yanzu ke aikin wanzar da zaman lafiya a Afirka (Ibrahim)