Taron na FOCAC da za'a yi shi a cibiyar Sandton dake birnin Johannesburg tsakanin ranakun 4 zuwa 5 na watan gobe wato Disamba zai yi amfani da taken: Afrika-Sin cigaba tare, bisa hadin gwiwwar moriyar juna don cimma buri daya.
Kamar yadda Ministar hulda kasashen waje da hadi kai Maite Nkoana-Mashabane ta yi bayani a wani taron manem labarai a Pretoria, ta ce a bayyane yake cewa taron koli na FOCAC na Jonnesburg zai daga matsayin huldar dake tsakain Sin da Afrika zuwa wani sabon matsayi, wanda zai amfani dukkan bangarori ya kuma yi tasiri a muradun cigaba na nahiyar.
Taron na FOCAC in ji ta, zai bude sabuwar dama ga Sin da Nahiyar ta Afrika a fannin hadin kansu. Sannan kuma taron zai ba da damar kara yunkurar da bunkasuwa, ya kuma bude wassu kofofi na ciniki da sauran batutuwa tsakanin bangarorin biyu.
Ministar ta yi bayanin cewa, ana sa ran shugabannin kasashe da na gwamnatocin Afrika, wakilai daga kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU, shugabannin hukumomin yankuna da sauran kungiyoyi na duniya duk za su halarci taro.
Madam Maite Nkoana-Mashabane ta ce, a lokacin taro, ana sa ran har ila yau a amince da yarjejeniyar Johannesburg da tsarin da zai fitar wanda ake sa ran zai shirya matakai na musamman da ake ganin zai taimaka wajen raya zumuncin na hadin gwiwwa da mutunta juna tsakanin Sin da Afrika.
Daga cikin wadannan matakai, akwai zurfafa hadin gwiwwa a bangarorin samar da kayayyakin more rayuwa, rage basussuka, samar da masana'antu, zuba jari, duba yadda za'a fadada kasuwanci, aikin noma, kimiyya da fasaha, kiwon lafiya, ilimi da kuma musanyar al'umma da al'adu.(Fatimah Jibril)