in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Darektan Jaridar "Le Democrate" ta Guinea-Bissau ya jaddada haskakawar huldar dangantakar Sin da Afrika
2015-11-09 10:15:25 cri
Darektan Jaridar "Le Democrate" ta kasar Guinea-Bissau, Antonio Nhaga, ya jaddada cewa huldar dangantaka dake tsakanin Sin da Afrika ta fi haskakawa fiye da dangantakar dake tsakanin Afrika da bankin duniya da asusun IMF, a cikin wata hira tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Jaridar "Le Democrate" na daya daga cikin manyan jaridun da aka fi karantawa a Guinea-Bissau. Kuma jaridar ta fi nazari yawancin lokaci kan dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika.

A cewar darekatan wannan jarida, Sin na taka muhimmiyar rawa wajen cigaban tattalin arzikin nahiyar Afrika.

Kasar Sin yanzu na yin abin da bankin duniya da IMF suka kasa yi, wato kawo gyare gyare kan tattalin arziki, in ji mista Antonio Hhaga.

Haka kuma, ya nuna cewa taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika wato FOCAC da zai gudana a cikin watan Disamba a kasar Afrika ta Kudu zai shimfida hulda mai karfi domin kara janyo taimakon kasar Sin.

Antonio Nhaga ya bayyana kuma cewa dangantakar kasar Sin na kara haskakawa a nahiyar Afrika, musamman ma a fannonin ababen more rayuwa, kiwon lafiya da kasuwanci.

Kasar Sin ta taimaka sosai wajen rage kangin talauci a Afrika, ta hanyar sayarwa al'ummomin kasashen Afrika da kayayyakin amfanin yau da kullum masu rahusa, in ji darektan Jaridar "Le Democrate". (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China