Mista Bergin ya bayyana cewa wannan haduwa ta manyan jami'ai, da zata samu halartar manyan shugabannin siyasa da masu bincike daga kasar Sin da kuma Afrika, za ta zama muhimmin ginshiki a cikin huldar dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika.
Dangantakar Sin da Afrika na taimakawa sosai wajen karfafa bada kariya ga manyan numan daji na nahiyar Afrika, in ji shugaban AWF.
A cewar jami'in, tsare tsaren hadin gwiwa na Sin da Afrika domin ingiza bada kariya namun dajin Afrika sun cigaba da karuwa a 'yan shekarun bayan bayan nan dalilin niyyar siyasa daga bangarorin biyu.
Haka kuma, ya nuna cewa wasu jerin taruka tsakanin Sinawa da 'yan Afrika sun gano wasu hanyoyin kara azama ga kokarin bada kariya ga nau'o'in namun daji a nahiyar. Inda ya kara da cewa kungiyoyin kare namun daji sun nuna gamsuwa da burgewa kan matakan da shugabannin Sin da na Afrika suke dauka domin bunkasa aikin bada kariya ga namun daji, tare da bayyana fatansu na ganin an cigaba da irin wadannan ayyuka na kare namun daji.
Akwai kwarin gwiwa wajen ganin cewa za a tattauna batun kare namun daji a taron koli na FCSA. Wannan shi ne abu guda mai muhimmaci, in ji mista Berjin. (Maman Ada)