Jakadan kasar Sin a kasar Zambia Yang Youming, ya ce, dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, ya bude wani sabon babi game da dangantakar sassan biyu.
Mr. Yang, wanda ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labaru a birnin Lusaka, fadar mulkin kasar Zambia, gabanin bude taron FOCAC da za a gudanar a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu a wata mai zuwa, ya kara da cewa, dandalin na ba da damar tattaunawa, da musayar ra'ayoyi tsakanin sassan biyu, matakin da ke karfafa hadin gwiwar sassan yadda ya kamata.
Jakadan na Sin ya kuma jaddada kudurin kasarsa na tallafawa nahiyar Afirka, wajen magance manyan matsalolinta, wato batun karancin ababen more rayuwa, da kuma karancin kwararru.
Bisa alkaluman kididdiga, ya zuwa shekarar bara, kudaden kasuwanci tsakanin Sin da Afirka sun zarta dala biliyan 220, yayin da kuma jarin da sassan biyu suka zubawa juna ya haura dala biliyan 30, adadin da ya karu matuka sama da na shekarar 2000, lokacin da aka kafa dandalin na FOCAC.
Kaza lika hannun jarin kasuwancin Sin a nahiyar Afirka shi ma ya karu daga kaso 3.82 bisa dari zuwa kaso 20.5 bisa dari a tsahon wannan lokaci.(Saminu)