Wannan na'ura tana daya daga cikin muhimman na'urorin da ake amfani da su wajen gudanar da nazari, baya ga warware matsaloli daban daban ta fuskar tattalin arziki, da kimiyya da fasaha. Sabili da haka, ake kallon na'urar da muhimmanci sosai a fannin daukaka matsayin kasa, musamman ma a fannonin karfin tattalin arziki da na kimiyya da fasaha.
Jerin manyan na'urori masu kwakwalwa da aka gabatar a wannan karo ya sheda yadda aka gaza samun canji kan fasalin kasashen duniya wajen mallakar na'urori. Har yanzu akwai gibi tsakanin kasar Sin, da kasar Amurka, wadda ta mallaki mafi yawan irin wadannan na'urorin.
Bayanai na cewa, yawan manyan na'urori masu kwakwalwa da kasar Amurka ta mallaka ya kai guda 233, sai kuma kasashen Sin, Japan, Birtaniya, Faransa, da kuma Jamus da ke biye da ita. (Bello Wang)