Kumbon a cewar babban injiniya dake jagorantar sashen sufurin kunbuna masu dauke da bil'adama na kasar ta Zhou Jianping, zai yi aiki ne tare da wani kumbon sufurin 'yan sama jannati da za a harba a farkon shekarar ta 2016.
Mr. Zhou ya ce babban kumbon dakon zai kunshi kayayyakin bukata na 'yan sama jannati da na ayyukan bincike, da na gyaran na'urorin kumbon bincike na Tiangong-2 da tuni ke sararin sama.
Ya ce fasahar harba kumbon dakon kaya na da matukar muhimmanci ga ayyukan binciken sama-jannati, don haka ya zama wajibi ga kasar Sin ta kara kwazo wajen lakantar wannan fasaha, musamman a kokarinta na kafa tashar binciken sararin sama ta kashin kan ta.
Mr. Zhou wanda kuma mamba ne a kwamitin koli na dandalin ba da shawara kan harkokin siyasar JKS, ya kara da cewa shirin kafa tashar mallakar kasar Sin wanda ake da burin aiwatarwa nan da shekarar 2022, za ta zamo abar alfaharin kasar, zai kuma lashe biliyoyin daloli kafin kammalar ta.
Bisa shirin da ake da shi za a harba kumbon dakon kaya na Tianzhou-1 ne bisa wata roka kirar zamani da a kaiwa lakabi da March-7. An ce mai yiwuwa za a gudanar da wannan aiki ne ta wata tashar harba kumbuna dake lardin Hainan dake kudancin kasar ta Sin.
Rohotanni sun bayyana cewa tuni aka yi nisa da aikin kirar rokar ta March-7. (Saminu Hassan)