in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mambobin kwamitin IOC 85 za su kada kuri'un zabar birnin da zai karbi bakuncin gasar Olympics ta lokacin sanyi a shekarar 2022
2015-07-31 13:45:26 cri
Kwamitin harkokin wasannin Olympics na duniya IOC, ya ce mambobin sa 85 ne za su jefa kuri'u, domin zabar birnin da zai dauki bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022. Bisa ka'idar zaben, birnin da ya samu fiye da rabin kuri'un da aka kada ne zai zamo mai masaukin bakin wannan gasa.

Bisa ka'idojin kwamitin, wakilan kasashen dake neman karbar bakuncin gasar, ba su da izini na jefa kuri'u. Don haka membobin kwamitin IOC guda 3 daga kasar Sin, ba za su jefa kuri'un su ba. Har wa yau shugaban kwamitin IOC Thomas Bach, shi ma ba zai jefa ta sa kuri'a ba.

Bisa ajandar da aka tsara, tsakanin karfe 5 da rabi zuwa 6 na yammacin yau Juma'a bisa agogon Beijing, za a gudanar da bikin sanar da birnin da ya samu izinin daukar bakuncin gasar, inda shugaban kwamitin IOC Bach zai sanar da sakamakon zaben da aka yi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China