A jawabin da ta gabatar, Michelle ta ce nakasassu na dunkule al'ummar duniya sama da komai. Ta ce ita da mai gidan ta na matukar alfahari da nakasassun masu wasannin motsa jiki.
Tun dai lokacin bazara na shekarar 1984 ne aka fara gudanar da gasar Olympics ajin nakasassu, wadda ta zamo babbar gasar kasa da kasa da birnin Los Angeles ya taba karbar bakunci a tarihi.
A bana 'yan wasa 6,500 ne daga kasashe da yankuna 165 ake sa ran za su halarci gasar, inda za su fafata a neman lambobin yabo 25.
Tuni dai kasar Sin ta tura tawagar ta mai kunshe da mutane 126, ciki hadda 'yan wasa 93, wadanda za su shiga rukunin wasanni 69, a jimillar manyan rukunonin wasanni 10. Wadannan wasanni sun hada da linkaya, da kwallon kwando, da kwallon kafa, da kwallon tebur, da dai suaran su.
Da yake karin haske game da matsayin kasar Sin a fannin gasar Olympics ta nakasassu, jakadan kasar na wasannin na Olympics Liu Tao, ya ce ya zama wajibi a nunawa masu nakasa kauna, kuma hakan na samuwa da zarar an maida hankali ga wasannin Olympics irin na nakasassu. Mr. Liu ya kara da cewa, baiwa wannan fanni kulawa tamkar samarwa nakasassu karin dama ce, ta kusanci da sauran al'umma, ta yadda za su kara jin kwarin gwiwar gudanar da kyakkyawar rayuwa mai cike da annashiwa.
Gasar Olympics ajin nakasassu, gasa ce da ke gudana a duk shekaru biyu biyu, ana kuma sauya lokutan ta daga bazara zuwa lokacin hunturu.
A shekarar 2007 an gudanar da wannan gasa ne a lokacin bazara a birnin Shanghai na nan kasar Sin.(Saminu Alhassan)