Forfesa Agyei-Mensah, maitaimakin shugaban jami'ar Ghana, yayi wannan sanarwa a yayin wani zaman taro na Afrika da Asiya da ya gudana baya bayan nan a birnin Accra.
A cikin wannan duniya ta gogayya, kowa ce kasa kuma kowa ne yankin ba zai yi takara shi kadai ba, don haka yana da kyau a samu fahimtar juna, in ji mista Agyei-Mensah.
Kasashen Asiya na bukatar fahimtar Afrika kana su ma 'yan Afrika suna bukatar fahimtar Asiya. Ina fatan wannan zaman taro zai ingiza burin da muke fata, in ji Forfesan.
Ya nuna cewa muhimman sauye sauyen cigaban da yankin Asiya ya samu a fannoni daban daban sun taimaka wajen shimfida wasu jerin tsare tsare na bincike da bada ilimi, da ma wasu kungiyoyin nazari na siyasa a cikin wannan duniya dake neman sanin ma'aunin al'ajabin damisan Asiya.
Misalai na Asiya game da samun cigaban tattalin arziki cikin sauri da cigaba mai karko, 'yan Afrika na ganinsu a koda yaushe, amma yana da kyau 'yan Afrika su yi nazarin wadannan abubuwan al'ajabi da dukkan abubuwa masu kyau da maras kyau domin ganin abin yin koyi da shi, in ji mista Agyei-Mensah.
Haka kuma, wannan cibiya ta nazarin yankin Asiya, zata kasance wani dandali domin samun ilimin da ya dace da fara gudanar da musanya tsakanin masana da daliban Asiya, in ji Forfesa Agyei-Mensah. (Maman Ada)