Matakin nada manufar taimaka wa kokarin da ake yi a fadin kasar na fuskantar barazanar leda. Dukkan kayayyakin leda da suka wuce girman ma'aunin micron 20 da 30 zasu fuskanci matakin hana amfani dasu. Matakin an dauke shi a ranar Alhamis a yayin wani zaman taro tsakanin ofishin ministan muhalli da masu kasuwancin ruwa cikin leda domin cimma hanyar da za a bi wajen kula da bolar ledodi.
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya bukaci kamfanoni da masu sarrafa leda da su dauki matakan da suka dace domin bada martani mai kyau kan barazana ga muhalli ko kuma su fuskanci hukuncin hana su yin amfani da ledodi.
Matakin hana yin amfani da wasu nau'o'in ledodi na daga cikin bukatun da kwamitin aiki ya gabatar wa gwamnati tun cikin shekarar 2010, amma aka kasa aiwatar da shi.
Ministan muhalli, Mahama Ayarigah, ya bayyana cewa matakin karshe za a cimma masa a cikin makwanni biyu ko uku.
Wasu kudurorin da gwamnatin kasar ke duba wa sun hada da kafa wani kwamitin sa ido na Eco-Brigade da ke kunshe da mutane dubu 10 domin yin aiki a birane, a bakin ruwa inda aka fi samun gubacewar muhalli dalilin ledodi. (Maman Ada)