Saif Rubie a cikin hirar da ya yi da BBC ya ce rashin dabaru a cikin wasan shi ne kadai dalilin da ya sa alkalin wasan ya gagara zama a cikin kasar domin sa ido a wasannin da 'yan kwallon ke yi.
Hukumar ta GFA a cikin wata sanarwa ranar Jumma'an nan ta ce wasannin premier da sauran wasannin cikin gida na dauke da 'yan wasa masu hazaka sosai inda wadansunsu suka koma buga ma manyan klob a kasashen Turai.
Ya yi misali da Baba Abdulrahman wanda a lokacin wasanni biyu kadai yake buga ma kungiyar Asante Kotoko a cikin gida amma kwanan nan ya rattaba hannu don buga ma kungiyar Chelsea na Ingila, daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya.
Hukumar ta GFA ta ce duk da cewar gaskiya ne daya daga cikin kalubalen da suke fuskanta shi ne yawan 'yan wasa, gazawar alkalan wasan kungiyar ta kasa wajen sa ido a zakulo masu hazaka daga cikin 'yan wasan na cikin gida shi ya kawo cikas.
Hukumar ta kuma ce 'yan wasan za su samu kwarin gwiwwa na dadewa suna wasa a Ghana idan alkalan wasa na kasar baki daya suka maida hankali a kungiyoyin wasannin. (Fatimah Jibril)