in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a ciyar da dauwamammen zaman lafiya da ci gaba a yankin Asiya ta gabas gaba, in ji firaministan kasar Sin
2015-11-22 16:48:44 cri
A jiya Asabar 21 ga wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron shugabannin kasar Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya, watau ASEAN karo na 18 da aka yi a cibiyar taron kasa da kasa dake birnin Kuala Lumpur na kasar Malaisiya. Kuma shugabannin kasashe 10 na kungiyar sun halarci taron.

A cikin jawabin da ya bayar, Li Keqiang ya ce, ya kamata kasar Sin da kungiyar ASEAN su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa fahimtar juna, samun ci gaba cikin hadin gwiwa da kuma rage sabanin dake tsakaninsu yadda ya kamata domin cimma burin kafuwar gamayyar tattalin arziki ta Asiya ta gabas a shekarar 2020, ta yadda za a iya ciyar da dauwamammen zama lafiya da ci gaba a yankin Asiya ta gabas gaba.

Haka kuma, ya ba da shawara guda shida domin ganin yadda za a iya cimma wannan buri, da farko, a inganta tsarin hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar ASEAN, na biyu, a kyautata hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, na uku, a daidaita shirin neman bunkasuwa ta kasashen dake yankin daya bisa shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, na hudu, a habaka aikin hadin gwiwa ta fannonin ginawar kayayyakin more rayuwa da kuma raya masana'antu a tsakanin kasa da kasa, na biyar, a karfafa hadin gwiwa kan ayyukan kiyaye tsaro, na shida, a dukufa wajen cimma dauwamammen ci gaba a yankin.

Kaza lika, Li Keqiang ya jaddada cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kungiyar ASEAN na da makoma mai kyau, kasar Sin na fatan cigaba da maimaita kyakkyawan zumuncin dake tskaninta da kasashen kungiyar, domin samun wadata tare da kuma ba da gudummawa ga zaman lafiya da ci gaba a yankin Asiya ta gabas har ma a duk duniya baki daya.

Bugu da kari, shugabannin kasashen kungiyar ASEAN sun nuna yabo matuka kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da kungiyar, suna kuma ganin cewa, bunkasuwar Sin na ba da taimako wajen tabbatar da zaman karko da ci gaba na wannan yanki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China