in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan cimma manufofin da ta tsara a shirinta na raya kasa
2015-11-18 09:54:50 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta aiwatar da abubuwan da ta tsara cikin shirin ta na raya kasa na shekaru biyar-biyar yadda ya kamata don ganin ta cimma manufar da ta sanya a gaba ta samar da al'umma mai wadata ya zuwa shekara 2020.

Firaminista Li ya ce, idan har kasar Sin ta cimma wannan nasara, hakan zai taimaka mata tsallake rukunin kasa mai matsakaitan masu samun kudin shiga.

Mr Li ya bayyana hakan ne yayin taron rubuta kundin shirin kasar na raya kasa na 13 na shekaru biyar-biyar wato daga shekarar 2016-2020.

Ya kuma kara da cewa, kasar Sin ta tsara manufofin da ta ke son cimma a fannonin tattalin azriki, al'adu da kuma muhalli ya zuwa shekarar ta 2020, ciki har da shirin ninka yawan GDPn kasar na shekarar 2010.

Firaminista Li ya ce, kamata ya yi a ba da muhimmanci kan ayyukan da suka shafi fasahohin sadarwa da na'urori na zamani da sabbin masana'natun da za su karawa kasar tagomashi.

Ya kuma bayyana shirin da kasar ke da shi na kara karfin Internet, inganta bangaren sufuri, aikin gona na zamani, raya makamashi da kare muhalli da sauransu.

A watan da ya gabata ne dai aka gabatar da shirin raya kasar ta Sin na 13 na shekaru biyar biyar yayin cikakken zama na 5 karo na 18 na kwamitin tsakiya na JKS.(Yaya Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China