in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin Li Keqiang ya gana da Bill Gates
2015-11-13 09:33:28 cri

Firayin ministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da hamshakin attajirin nan 'dan kasar Amurka Bill Gates a birnin Beijing a ranar Alhamis din nan.

Mista Li, ya ce, gwamntin kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashen duniya domin tunkarar matsalar sauyin yanayi da kuma tsara shirin nukiliya mai tsabta a matsayin wata sahihiyar hanya da za ta rage matsalar dumamar yanayi a duniya.

Ya ce, gwamnatin kasar Sin tana fatan kamfanonin Amurka za su hada gwiwa da kamfanonin kasar Sin don yin aiki tare wajen samar da tsarin fasahar zamani, tare da gudanar da bincike na hadin gwiwa wanda zai kafa wani tsarin da za'a samu sauki wajen rage kashe kudade da inganta yanayin kamfanonin makamashi na kasar Sin.

Ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta goyi bayan dukkanin bangarorin biyu domin samar da hadin gwiwa kan batun shirin na nukiliya, ta yadda za su samu karbuwa a kasuwannin duniya da kuma samar da dawwamamman ci gaba.

Bill Gates, ya yabawa kasar Sin dangane da kokarinta na tunkarar matsalar sauyin yanayi da samar da sabbin kamfanonin makamashi.

Ya kara da cewa, hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, zai taimaka wajen samar da ci gaban fasahar zamani a masana'antun dake samar da makamashi mai araha a duniya wanda zai taimakawa kasashe masu tasowa su samu ci gaba. (Ahmed Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China