in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan kara hadin gwiwa da kasar Faransa
2015-11-03 20:00:51 cri

Firaministan kasar Sin Mista Li Keqiang, ya gana da shugaban kasar Faransa Francois Hollande wanda yake ziyarar aiki a nan birnin Beijing, a yammacin ranar Talatar nan.

Yayin ganawar tasu, Mista Li ya ce, Sin na fatan kara yin kokari da Faransa a fagen rika zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da sa kaimi ga hadin kai kan wasu manyan ayyuka da sabbin sana'o'i, da kyautata yin mu'amala ta fuskar al'adu, a kokarin raya dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata.

Ban da wannan kuma, Mista Li ya jaddada cewa, Sin na fatan kara hadin gwiwa da kasashen duniya ciki hadda Faransa, game da batun sauyin yanayi, don sa kaimi ga cimma matsaya daya, da kulla wata yarjejeniya cikin daidaito da inganci a yayin taron sauyin yanayi da za a yi a birnin Paris, bisa ka'idar daukar nauyi baki daya cikin adalci tare da sanin bambanci, da ka'idar daidaito gwagwadon karfin ko wace kasa, ta yadda za a samu ci gaba mai dorewa yayin da ake daidaita sauyin yanayi yadda ya kamata.

A nasa bangare, Mista Hollande ya ce, Sin da Faransa na da fifiko a fannonin makamashi na bola jari, da kuma sana'ar kiyaye muhalli da tsimin makamashi, bangarori ne guda biyu dake da makoma mai kyau ta fuskar hadin kansu, da kuma cimma moriya mai inganci.

Shugaban na Faransa ya kuma yi imani da cewa, Sin za ta ba da gudummawa mai ma'ana a game da taron sauyin yanayi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China