in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya halarci taron kolin masu masana'antu da 'yan kasuwa karo na 5 na Sin da Japan da Koriya ta Kudu
2015-11-02 10:53:49 cri
A jiya Lahadi da safe, firaministan kasar Sin Li Keqiang, shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye, firaministan kasar Japan Shinzo Abe suka halarci taron kolin masu masana'antu da 'yan kasuwa karo na 5 na Sin da Japan da Koriya ta Kudu.

A yayin taron, Li Keqiang ya bayyana cewa, bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana ita ce tushen inganta hadin gwiwar dake tsakanin uku. Ya kamata a koyi fasahohi daga tarihi, fuskantar makoma, bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da kuma warware matsaloli yadda ya kamata yayin da ake yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen uku. A cikin shekaru 16 da suka gabata, yawan cinikayya a tsakanin Sin da Japan da Koriya ta Kudu ya karu da kashi 12 cikin dari a kowace shekara, kasashen uku sun kasance muhimman abokan cinikayyan juna.

Bunkasuwar tattalin arziki a tsakanin kasashen uku da kyautatuwar tsarin sana'o'insu, za su kara bunkasa hadin gwiwar tattalin arzikin juna, kana hakan zai taimaka ga samun bunkasuwa a yankin Asiya har ma a dukkan duniya baki daya.

Li Keqiang ya yi nuni da cewa, Sin ta bada shawara kan yadda za a inganta hadin gwiwar kasashen uku.

Na farko, a fadada cinikayya da bude kasuwa da juna, kara yin hadin gwiwa a fannonin jigilar kayayyaki, kwastam, sa ido ga ingancin kaya da dai sauransu don samar da yanayi mai 'yanci da sauki yayin da ake gudanar da harkokin ciniki. Na biyu, a bullo da sabbin ayyukan zuba jari da hadin gwiwa a tsakaninsu. Na uku, a fadada yin hadin gwiwa a tsakani a fannin samun bunkasuwa ba tare da gurbata yanayi ba. Na hudu, a kara yin hadin gwiwa kan ayyukan kirkire-kirkire. Na biyar, a inganta hadin gwiwarsu a fannin al'adu, da yin kokari tare don cimma burin musaya a tsakanin al'ummomin kasashen uku da yawansu ya kai miliyan 30 ya zuwa shekarar 2020. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China