An gudanar da gagarumin taro a harabar fadar Potala dake birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta, domin murnar cikar jihar shekaru 50 da kasancewa mai cin gashin kanta. Dubban al'ummar jihar sun yi gangami a wannan fada, inda suka rika daga tutoci suna shewa da nuna farin ciki, kai ka ce bikin sabuwar sheka suke gudanarwa.
An dai tabbatarwa jihar Tibet ikon cin gashin kai ne a shekarar 1965, bayan kaddamar da majalissar wakilan al'umma, da wakilan kananan hukumomi, matakin da ya nuna cewa, al'ummar jihar na da damar zabar wakilansu a majalissar al'umma.
An gudanar da maci tare da kade-kade, da wake-wake, tare da raye-raye masu ban sha'awa, wanda dakarun soji da jami'an gwamnati da kuma fararen hula sama da 6,000 suka gudanar.(Saminu)