Babban Sakataren MDD Ban Ki-moon, ya yi Allah wadai da mummunan harin kunar bakin wake na ranar Talatar nan wanda ya yi sanadiyyar hallaka rayuka da jikkata mutane masu yawa a garin Yola a arewa maso gabashin Najeriya.
Harin wanda ya hallaka mutane 32, sannan wasu 80 suka samu raunuka, an dasa bam din ne a wata tashar mota da misalin karfe 8 na yammacin ranar Talatar, a dai dai lokacin da jama'a suka taru don cin abincin dare.
Mista Ban ya aike da sakon ta'aziyya ga gwamnatin Najeriya da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon harin, tare da yin addu'ar samun sauki ga wadanda suka jikkata.
Babban sakataren ya ce, babu wani tsari da ya amince da kashe rayukan al'umma da ba su ji ba, ba su gani ba, sannan ya kara da cewa, MMD a shirye take ta taimaka wa Najeriya domin yakar ayyukan ta'addanci. ( Ahmad Fagam)