in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara damke wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne a Najeriya
2015-11-19 10:14:21 cri
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa, jami'an tsaro da ke fafatawa da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, sun yi nasarar damke karin mutane biyu da mahukuntan kasar ke nema ruwa a jallo.

Wata sanarwa mai dauke da sanya hannun kakakin rundunar sojojin kasar Kanar Sani Kukasheka Usman, ta bayyana cewa, an damke Abubakar Sadiq da Mohammed Usman ne a jihar Borno mai fama da hare-haren mayakan Boko Haram.

Sanarwar ta ce, sunayen mutanen biyu da aka kama su ne na 28 da kuma na 40 cikin jerin mutane 100 da rundunar sojojin kasar ta fitar a watan da ya gabata a matsayin wadanda suka kitsa hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaddamarwa a sassan kasar.

Bugu da kari, sanarwar ta kara da cewa, kama wadannan mutane wata babbar nasara ce ga hukumomin tsaron kasar da ma daukacin jama'a a yakin da dakarun kasar ke yi da 'yan ta'adda da masu tayar da kayar baya a Najeriya.

A nasa jawabin babban hafsan mayakan kasa na Najeriya Laftana janar Tukur Buratai, ya yaba kokarin sojoji da 'yan sanda na ganin bayan 'yan ta'adda a kasar.

Kamen mutanen biyu na ranar Laraba na nuna cewa, yanzu haka an kama mutane 5 ke nan cikin 100 da sojojin kasar ke nema ruwa a jallo. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China