in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun tarwatsa wurin da Boko Haram ke kera rokoki
2015-11-19 10:22:16 cri
Rundunar sojojin Najeriya ta ce, ta yi nasarar tarwatsa wani wurin da mayakan Boko Haram ke kera makaman roka, yayin wani samane na musamman da dakarunta suka kaddamar a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya, kanar Sani Kukasheka Usman, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai cewa, sojojin sun kaddamar da samamen a ranar Talata ne a yankin Delwa da ke gundumar Borno.

Sanarwar ta kara da cewa, wannan nasara da sojojin suka samu kan mayakan na Boko Haram ya dakushe kaifin mayakan na kera rokoki da makaman harba rokokin da suke amfani da su wajen halaka fararen hula.

Babban hafsan mayakan kasa na Najeriya Laftana janar Tukur Buratai ya bayyana nasarar da dakarunsa suka samu a matsayin wani mataki na kawo karshen kungiyar baki daya.

Janar Buratai ya bukaci dakarun da ke yaki da mayakan Boko Haram da su kara jajurcewa a yakin da suke na ganin bayan kungiyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China