Da ya ke yiwa taron manema labarai karin haske game da sabon tsarin a birnin Legas cibiyar kasuwancin kasar, darektan hukumar ta NSE Ade Bajomo ya ce, hukumar ta dauki wannan muhimmin mataki ne ta yadda tsarin hada-hadar hannayen jarin kasar zai dace da matsayin kasa da kasa.
Ya ce, sabon tsarin hada-hadar zai baiwa 'yan Najeriya da sauran masu sha'awar zuba jari damar zuba dukiyarsu a kasuwannin hannayen jari ta wayoyinsu na salula ba tare da wata fargaba ba.
Darektan ya shaidawa manema labarai cewa, sabon tsarin hada-hadar hannayen jari ta wayar salulan zai karawa tsarin cinikayyar hannayen jari martaba da kuma saukin shiga kasuwannin.(Ibrahim)