in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya rantasr da ministoci
2015-11-11 20:35:29 cri

A yau ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya rantsar da majalisar ministocinsa, watanni shida tun bayan da ya kama aiki a watan Mayun wannan shekara.

A jawabinsa yayin bikin rantsar da sabbin ministocin da ya gudana a fadar shugaban kasar da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, shugaba Buhari ya ce, yana da tabbacin a kansu don haka ya bukace su da su zage damtse don ciyar da kasar gaba.

Shugaba Buhari ya zauna da ministocin a karon farko, jim kadan bayan ya sanar da ma'aikatun da za su rike. Koda ya ke kamar yadda ya nanata tun farko, shi ne zai shugabancin ma'aikatar man fetur ta kasar, bayan da ya nada Ibe Kachikwu a matsayin manajan darektan kamfanin man fetur na kasar.

A jiya ne dai Shugaba Buhari ya sallami manyan sakatarorin kasar guda 17, a wani mataki na yin garambawul ga ayyukan gwamnati. Kuma nan take ya maye gurbinsu da wasu 18.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China