in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotannin shirin mayakan Boko Haram na kai wasu hare-hare
2015-11-16 09:47:30 cri
Mahukuntan Najeriya sun karyata rahotannin cewa, mayakan Boko Haram suna shirin kaddamar da hare-hare a jihohin da ke kudu maso yammacin kasar.

Kakakin hedkwatar tsaron kasar Kanar Rabe Abubakar wanda ya bayyana cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ya ce, rahotannin da ake yayatawa ba su da tushe balle makama.

Kanar Abubakar ya kara da cewa, hare-haren baya-bayan nan da dakarun kasar suka kaddamar a yankin arewa maso gabashin kasar da ke fama da hare-haren mayakan na Boko Haram sun karya lagon 'yan tawayen wadda ya sa hakan zai yi matukar wahala su iya shirya kai wasu hare-hare a sassan kasar.

Bugu da kari, jiga-jigan kungiyar da aka kama, ya rage kaifin kungiyar na kaddamar da duk wasu hare-hare.

Don haka ya bukaci jama'a da su taimakawa hukumomin tsaro da muhimman bayanai tare da kai rahoton duk wanda ba su amince da take-takensa ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China