Shedun gani da ido da jami'an tsaro sun ba da tabbacin mutuwar mutane a kalla 50 sakamakon wani harin kunar bakin wake da wasu mata 2 suka kai a ranar Larabar nan a kasuwar sayar da wayar hannu a jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya.
Jami'in hukumar 'yan sandan jihar Kano Musa Katsina, wanda ya ziyarci wajen da abin ya faru, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua faruwar lamarin, sai dai bai bayyana adadin mutanen da harin ya rutsa da su ba, ya ce, suna ci gaba da bincike.
Saleem Ahmed Saleem, wanda ya gane wa idonsa afkuwar lamarin, ya ce, harin ya faru ne a daidai lokacin da jama'a suka taru don gudanar da sallar la'asar, kuma a cewarsa, mutane sama da 50 ne suka mutu a sakamakon harin
Shi ma Mohammed Garba ya ce, bam na farko ya tashi ne a kofar shiga kasuwar, yayin da bam na biyu ya tashi a tsakiyar kasuwar.
Garba ya kara da cewa, akwai yiwuwar samun karin wadanda harin ya rutsa da su bayan jami'an aikin ceto sun kammala gudanar da aikinsu.
Wata 'yar kasuwa mai suna Hajia Maikudi ta ce, an kwashe sassan jikin mutane masu tarin yawa a jakakkunan leta wadanda boma boman suka tarwatsa.( Ahmad Fagam)